CAN reshen arewacin gida Najeriya ta ce tabarbarewar tsaro da kuma matsin tattalin arziki ya jefa miliyoyin yan Najeriya cikin yunwa da talauci.
Kungiyar ba ta ga alfanun bikin ranar demokradiyya ba da aka yi a ranar 12 ga watan Yuni, la’akari da yadda ake ci gaba da satar dalibai da kuma hana manoma shiga gonakinsu, wanda kungiyar tace zai haifar da yunwa a nan gaba.


Kamar yadda BBCHausa ta samo daga Jaridar The Nation ta ambata cewa kakakin kungiyar reshen arewa, Rabaran Jechonia Albert na cewa ”CAN ta damu da yadda hare-hare ke karuwa a makarantu, da kuma satar dalibai musamman a jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara da kuma Neja.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: