Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ya ce birnin Zariya na cikin tsaka mai wuya.

Sarkin ya bayyana hakan ne a yau Litinin lokacin da ya karbi bakuncin tawagar Shugabannin Tsaro karkashin jagorancin Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan.

Sarkin ya ce mazauna birnin ba sa samun barci da ido a rufe saboda sace-sacen mutane da ake yin don neman kudin fansa a cikin birnin da kewayensa.

Ya bayyana yanayin a matsayin wanda ba za a amince da shi ba, tare da yin kira ga gwamnati da ta dauki mataki.

Alhaji Nuhu Bamalli ya ce duk da cewa akwai cibiyoyin tsaro kamar makarantar horar da sojoji a yankin masarautar tasa, amma al’ummarsa na zaune cikin fargaba.

Shi kuwa Kwamishina Aruwan cewa yayi sun je fadar ne don kara samun kwarin gwiwa tare da jajantawa masarautar kan harin da aka kai Nuhu Bamalli Polytechnic da wasu kauyuka makwabta.

Ya ce gwamnati na yin bakin kokarinta don kare masarautar da jihar baki daya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: