Rundunar yansandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane biyu a wani hadari akan titin Hadejia zuwa Kano a yankin karamar hukumar Ringim.


Mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar yansandan jihar Jigawa, ASP Shisu Adam, ya shaidawa manema labarai cewa hadarin ya auku a jiya da misalin karfe 11 na safe.


ASP Adam yace hadarin ya auku ne bayan an yi taho mu gama tsakanin wata mota kirar Honda da wani babur.


Yayi bayanin cewa bayan taho mu gamar, matukin babur din da wani fasinja da yake goyo sun samu munanan raunuka inda aka garzaya da su zuwa babban asibitin Ringim domin a kula da lafiyarsu.

Jami’in hulda da jama’ar na yansanda yace daga baya wani likita a asibitin ya tabbatar da mutuwar mutanen.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: