Nasir El-Rufai Ya Ce Bai Saci Kobo A Baitul Malin Jihar Ba A Shekaru Takwas Da Ya Yi Yana Mulki

0 80

Gwamnan jihar Kaduna mai barin gado Nasir El-Rufai ya ce bai saci Kobo a baitul malin jihar ba a shekaru takwas da ya yi yana mulki.

Ya kalubalanci magabatan da su fito su rantse da Alkur’ani mai girma cewa ba su taba satar kudin gwamnati ba a lokacin da suke mulki.

Gwamnan ya mayar da martani ne kan sukar da ake masa bayan ya zargin tsohon Gwamna Ahmed Makarfi da mallakar wasu kamfanoni tara ba bisa ka’ida ba, inda ya nemo takardun rushe su.

Sai dai gwamnan mai barin gado ya ce wasu daga cikin magabata sun yi amfani da dukiyar jama’a da aka sace wajen gina gidaje a Kaduna da Hadaddiyar Daular Larabawa. Domin tabbatar da ikirarinsa na cewa bai arzuta kansa ba, El-rufai ya ce gidan da ya gina kafin ya zama gwamna daya ne, kuma a cikinsa zai bar mulki a ranar Litinin mai zuwa, ranar da wa’adin mulkin sa zai kare.

Leave a Reply

%d bloggers like this: