Cibiyar Dakile Cututtuka masu yaduwa ta Kasa NCDC, ta sanar da cewa Sabbin mutane 24 ne suka kamu da cutar korona a jiya Juma’a a ƙasar.

Hukumar NCDC ta ce sabbin kamuwar sun fito ne daga jihohi biyar ciki har da Abuja, babban birnin ƙasar, sannan kuma babu wanda cutar ta yi ajalinsa.

NCDC ta ce Jihohin su ne: Legas mai mutum 12, Gombe mai shida, sai kuma Abuja da Kaduna da Rivers masu biyu-biyu kowaccensu.

Ya zuwa yanzu, NCDC ta ce jumillar mutum dubu 167,051 ne suka harbu da cutar Corona a Kasar, akwai mutane 2,117 da cutar ta hallaka su, sannan an sallami mutane dubu 163,430 bayan sun warke daga cutar.

Kawo yanzu akwai mutane dubu 1,504 da suke cigaba da samun kulawar Likitoci a cibiyoyin da hukumar ta ware.

Tun bayan bayyana cutar a watan Fabreru na shekarar 2020, kimanin mutane Miliyan 2, da dubu 113,061 ne akayi musu gwajin cutar a kasa baki daya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: