NDLEA ta kama wani mutum da ya kasayar da hodar Iblis fiye da guda casa’in

0 80

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama wani magidanci mai shekaru 44, mahaifin ‘ya’ya 3, mai suna Gabriel Anthony, bisa laifin hadiyar kunshi 96 na hodar iblis, wadanda ya kasayar yayin da yake tsare a hannun hukumar.

Daraktan yada labarai da wayar da kai na hukumar, Femi Babafemi, ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya rabawa kamfanin dillancin labarai na kasa jiya a Abuja.

Babafemi yace Anthony wanda aka kama a filin jiragen sama na Nmandi Azikiwe dake Abuja a ranar Juma’a, 6 ga watan Nuwamban da ya gabata, dan asalin kauyen Nike ne a yankin karamar hukumar Enugu ta Arewa a jihar Enugu.

Yace an kama wanda ake zargin yayin bincike kafin tashin jirgi.

A cewarsa, wanda ake zargin ya taba zuwa kasar Jamus a shekarar 1996 tsawon shekaru 2 a matsayin mai neman mafaka, inda daga nan ya koma kasar Sifaniya a shekarar 1999.

Babafemi ya kara da cewa wanda ake zargin ya amince cewa ya karbi kwangilar safarar miyagun wanda za a biya shi euro dubu 1 da 500 idan ya samu nasarar kai hodar zuwa kasar Sifaniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: