NEDC ta kaddamar da harsashin ginin gidaje 500 a fadin Jihar Yobe

0 81

Hukumar Cigaban Yakin Arewa Maso Gabas tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Yobe sun kaddamar da harsashin ginin Gidaje 500 a fadin Jihar.

Da yake yiwa manema labarai Jawabi shugaban Hukumar Muhammad G Alkali, ya ce an kirkiri hukumar ne domin magance matsalolin da suke addabar cigaban yankin Arewa maso Gabas, tare da farfado da yankin wanda ya lalata tsawon shekaru 12.

A cewarsa, hukumar ta bukaci gwamnatin Jihar ta bata filin da zata gina gidaje 500 a fadin jihar.

Shugaban hukumar ya ce zasu gina gidaje 250 a birnin Damaturu, 50 a Buni Yadi, 50 a Patiskum, 50 a Gashua, 50, a Geidam da kuma wasu 50 din a karamar hukumar Nguru.

Hukumar ta kuma mika Kayayyakin Abinci da sauran kayan bukatu ga gwamnatin JIhar Yobe domin rabawa a jihar.

Kazalika, ya ce hukumar ta yaye Matasa 192 na rukunin na 2, wanda aka basu horo kan Fasahar Sadarwa a Jihar Yobe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: