Tsohon Firaministan kasar Ivory Coast ya rasu saboda cutar Korona

0 91

Kamfanin dillacin labarai na AFP ya ruwaito cewa Mista Charles Konan Banny, wanda ya taba riƙe muƙamin firaminista Ivory Coast daga 2005 zuwa 2007, ya mutu a asibitin birnin Paris bayan kamuwa da cutar korona.

Shugaba Alassane Ouattara ya bayyana alhininsa ga mutuwar Mr Konan Banny, mai shekara 78, yana mai cewa abokinsa kuma ɗan uwa ya yi wa ƙasa aiki wanda ya taka muhimmiyar rawa ga zaman lafiyar ƙasa.

Tsohon firaminista Guillaume Soro, wanda ya gudu daga ƙasar ya bayyana cewa Marigayin ya sauya tunaninsa kan siyasar Ivory Coast da kuma ƴan siyasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: