Shugaba Buhari ya bukaci ma’aikatan lafiya da su sake shawara kan yajin aikin da suke gudanarwa

0 86

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci Ma’aikatan Lafiya da suke fadin kasar nan su sake shawara kan yajin aikin da suke gudanarwa a yanzu haka.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Kakakin Shugaban Kasa Mista Femi Adesina ya rabawa manema labarai a Abuja, inda ya ce ya Kamata Ma’aikatan su kasance masu Fahimta.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a bayan ya gana da wakilan Kungiyar Likitoci ta Kasa, inda ya basu tabbacin cewa gwamnati zata biya dukkan hakkokin su.

Kungiyar Likitoci masu neman Kwarewa ta shiga yajin aiki a ranar 2 ga watan Agusta, biyo bayan abinda suka kira gazawar gwamnati wajen biyan su Albashin da ya kamata, yayin da a gefe guda kuma Kungiyar Likitoci da kuma Kungiyar Ma’aikatan Lafiya suke kokarin tafiya yajin aikin kamar yadda suka ayyana hakan.

Shugaba Buhari ya ce rayukan yan Najeriya da dama zasu salwanta a duk lokacin da likitoci suka ki kulawa da marasa lafiya, wanda hakan ya sa dole likitocin suyi sulhu da gwamnati.

Kazalika, ya ce hakkin kare rayukan yan Najeriya ba abu bane da ya ta’allaka akan gwamnati kadai abune da ya rataya akan kowa da kowa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: