Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawallen Maradun, ya bayyana matsayar gwamnatinsa na cewa bazata yi sulhu da yan bindiga ba, biyo bayan yadda suka barar da damar tuban da aka basu a baya.

Gwamna Bello Matawalle, ya ce gwamnatinsa tana tallafawa hukumomin tsaro wajen zakulo yan bindigar daga maboyar su, inda ya bukaci mutanen jihar su bada tasu gudunmawar.

Matawallen Maradun ya ce biyo bayan yadda hukumomin tsaro suke kashe su ne ya sanya suke neman sulhu da gwamnatin a yanzu haka.

Haka kuma ya ce wasu yan bindigar sun fara yin kwaura daga Zamfara zuwa Jihohin da suke makotaka da jihar, domin gujewa matakan da gwamnatinsa da kuma Sojojin suke dauka.

Gwamnan ya ce gwamnati zata hukunta duk Dan Siyasar da ta kama yana tallafawa yan bindigar.

A kwanakin baya ne hukumomi a jihar suka dauki matakan kakaba doka domin daina sayar da Abinci da Fetur da kuma sauran bukatu ga sansanonin yan bindigar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: