Jihar Jigawa ta mayarwa da maniyatan aikin Hajji da basu je ba kudadensu

0 65

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta mayarwa da maniyatan aikin Hajji 609 na shekarar 2020 da kuma 2021 da basu je aikin hajjin ba kudadensu kimanin naira miliyan dari bakwai da hamsin da biyu.

Sakataren zartarwa na hukumar na Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Sani Alhassan shine ya sanar da hakan a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Dutse babban birnin Jiha.

A cewarsa, hukumar Mahajjata ta Kasa NAHCON ta umarci hukumomin hukumar na Jihohi suyi gaggawar dawowa da Mahajjatan da basu je aikin ba kudaden su, biyo bayan umarnin da gwamnati Saudi Arabia ta bayar saboda cutar corona.

Haka kuma yace kimanin maniyata 1,165 ne suka biya kudadensu, inda daga ciki aka mayarwa da 609 kudadensu.

Alhaji Muhammad Sani Alhassan yakara da cewar a yanzu haka akwai kudaden maniyatan 2020 da 2021 su 556 da basu karbi kudadensu ba.

Kazalika, ya ce maniyatan da basu karbi kudadensu ba, su za a fara bawa kulawa ta musamman a aikin hajji mai zuwa.

Alhaji Muhammad Sani Alhassan yace a badi ba zasu karbi kudaden ajiya ba har sai an bada kason kujerun aikin hajjin bana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: