Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Bauchi ta kafa kwamatin mai mutane 19 domin fadakar da mutane kan rigakafin cutar Corona.

Sakataren Zartarwa na Hukumar Dr Rilwanu Muhammaed, shine ya kaddamar da kwamatin a jiya a birnin Bauchi.

Dr Rilwanu Muhammad, ya ce an kafa kwamatin ne, biyo bayan umarnin da hukumar Lafiya a matakin farko ta Kasa ta bayar kan fadakar da mutane dangane da rigakafin cutar covid-19 zagaye na biyu.

A cewarsa, wayar da kan mutanen yana da muhimmanci, domin sauya halayyar su da kuma sauya musu tunani domin su karbi sabon sauyi a jihar.

Kazalika ya ce kwamatin ya kunshe masu fadakar da mutane kan zuwan rigakafin, da lokacin rigakafin, da kuma bayan an yiwa mutane rigakafin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: