Fadar Shugaban Kasa ta ce an yiwa Jawabin shugaban Kasa Muhammadu Buhari mummunar Fahimta, wanda ya yi bayan ganawar sirri da Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma, da kuma shugabannin Kudu Maso Gabas.

An rawaito wurin da shugaba Buhari, bayan kammala jawabinsa, inda yake cewa zaiyi taka tsantsan a duk lokacin gwamnan Jihar ta Imo ya gayyace shi zuwa Jihar.

Kakakin Shugaban Kasa Mista Femi Adesina, shine ya bayyana hakan, inda yake cewa masu son tada zaune tsaye ne suke yada labaran saboda biyan bukatun kansu.

A cewarsa, a wurin taron Shugaba Buhari ya bayyana cewa ya gamsu da irin tarbar da aka masa, tare da mutanen da suka tarye shi a lokacin da ya kai ziyara zuwa yankin Kudancin Kasar nan, inda suka tattaunawa a tsakanin su a birnin Owerri.

Mista Adesina, ya ce Shugaba Buhari ya halarci Jihar ne, domin kaddamar da wasu ayyuka wanda gwamnan jihar ya aiwatar, kuma yayi mamakin irin yadda Dattawa 50 suka tarye shi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: