An bayyana Jihohin Bauchi, Borno, Kano, da kuma Kebbi a matsayin wuraren da aka fi samun masu satar Jarabawa a kasar nan.

Shugaban Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sikandire ta NECO Farfesa Dantani Wushishi, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da mukala mai taken Illolin satar Jarabawa.

Mista Wushishi ya ce shekaru 5 na baya satar amsar jarrabawa ta zama tamkar ba komai ba, musamman a Jihohin Bauchi, Borno, Kano, da kuma Kebbi.

Farfesa Wushishi, ya ce satar amsa a Jihohin ya zama tamkar ruwan dare, inda ake yi babu boyewa.

Haka kuma ya ce hakan yana da alaka da koma baya da yankin yake fuskanta a fannin Ilimi, wanda kuma hakan yake shafar masu karatun Digiri da suka fito daga yankin.

Kazalika, ya bukaci gwamnati ta dakatar da bada fifiko akan samun shaidar takardun maimakon kwarewa, domin dakile satar jarabawa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: