Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad, ya tallafawa matasa da mata su 1000 da kayan sana’a da kudade a kananan hukumomin ‘Bagoro da Tafawa Balewa dake jihar.

Gwamnan cikin bayanan yace,kimanin mutane 500 ne daga kowacce karamar hukumar suka amfana da wannna tallafin, inda yace 250 daga cikinsu an tallafa musu ne da kayayyakin da suka hada injin nika, keken dinki, babura masu kafa 2, yayin da sauran 250 daga kowacce karamar hukumar aka basu naira dubu 50 kowannensu.

Cikin bayanan gwamnan yayin mika kayan tallafin ga al,ummar kanannan hukumomin, yace sun bayar da wadadannna kayan tallafin ne ta cikin sabon shirin nan da yayi masa kalabi da suna ‘Tallafawa Da Farfado Da Tattalin Arzaki Daga Kaura’

Ya kara da cewa wannan shiri ne da aka shirya gabatar da shi a dukanin kananan hukumomi 20 dake jihar domin samarwa matasa ayyukan yi, kuma yanzu haka sn samu nasarar gabatar da wannan shirin a Kananan hukumomi 6 dake fadin jihar.

Bala Muhammad ya kara kara da cewa kafin bada wannan tallafin, saida suka bayar da bashin babura masu kafa 3 ga kimanin mutane 1000 a fadin jihar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: