Gwamnatin jihar Yobe zata samar da wuraren kiwo domin magance matsalar rikici tsakanin makiyaya da manoma

0 86

Gwamnatin jihar Yobe hadin gwaiwa da gwamnatin tarayya sun shirya samar da wuraren kiwo na zamani domin magance matsalar rikicin dake faruwa tsakanin Fulani makiyaya da manoma a fadin jihar.

A cewar shugaban cigaban kiwo na jihar Yobe Dr Idrissa Madaki tini wannan shirin yayi nisa tsakanin gwamnatocin 2, kuma sun kammala duba wuraren da za’agudanar da wadannan ayyukan a santoriya uku da ake da su a fadin jihar.

Madaki ya kara da cewa yanzu haka gwamanatin jihar Yobe ta kammala cire naira biliyan 12 wanda kaso 50 ne cikin 100 na kudaden da za’agudaanr da wadandan ayyukan, kuma nan bada dadewa gwamanatin tarayya zata bada sauran kaso 50 cikin 100 na kudaden.

Ya kara da cewa wannnan aikin bawa kawa kawo sasanto zaiyi tsakanin Fulani makiyaya da manoma ba, zai kuma habbaka fannin samar da amfanin ga manoma da makiyaya.

Anasa bangaren shugaban kungiyyar Kulen-Allah ta kasa Mohammed Bello Kalil ya bayyana gamsuwar da samar da wannan aikin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: