Gwamnatin Jihar Bauchi ta nanata kudurinta na sake bunkasa samun kudaden shiga ga Jihar

0 70

Gwamnatin Jihar Bauchi ta nanata kudurinta na sake bunkasa samun kudaden shiga ga Jihar.

Sabon Kwamishinan Ma’aikatar Kudi da Cigaban Tattalin Arziki na Jihar Bauchi Alhaji Modibbo Abdulkadir Ahmed, shine ya bayyana hakan a lokacin da ya shiga ofis domin jagorantar ma’aikatar.

Da yake jawabi a lokacin da yake ganawa da Ma’aikata da sauran Shugabannin Ma’aikatar Hon Ahmed ya ce biyo bayan halin da Jihar take ciki ya zama wajibi gwamnati ta dauki sabbin dabarun tattara kudaden shiga, domin cike gibin da gwamnatin jihar take samu daga gwamnatin tarayya.

Kwamishinan ya ce baya ga sake bunkasa kudaden shiga ga gwamnatin Jihar, Ma’aikatar zata yi hadin gwiwa da sauran masu ruwa da tsaki a fannin samar da kudaden shiga.

Kazalika, ya godewa gwamna Bala Muhammad, bisa bashi mukamin kwamishina, inda ya bada tabbacin cewa shugabancinsa zaiyi duk mai yiwuwa domin kaiwa ga Nasara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: