NPC Ta Bayyana Dalilin Da Yasa Ba Za’a Yi Tambayoyi Kan Addini Da Kabila Ba A Kidayar 2023

0 73

Hukumar kidaya ta kasa (NPC) ta bayyana dalilin da ya sa ba za a yi tambayoyi kan addini da kabilanci ba a kidayar 2023.

A wani jawabi a ranar Juma’a, hukumar ta ce tun lokacin da ta fara gudanar da aikin a shekarar 1991, ba a sanya wadannan tambayoyi domin batutuwa ne masu muhimmanci da za su dauke hankali daga bukatunta.

An ba da sanarwar ne a lokacin da Kwamitin Yaɗa Labarai na Ƙasa kan ƙidayar yawan jama’a da gidaje ta 2023 ya kai ziyara gidan talabijin na kasa da ke Kano.

Shugaban hukumar wayar da kan jama’a ta kasa Dr Garba Abari ne ya jagoranci ziyara, kuma an yi wannan karin haske ne sakamakon ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.

A cewar wani mamba a kwamitin, Dr Isiaka Yahaya, hukumar ba ta da bikatar sanin addini da yare na ‘yan kasa.

A wani labarin na daban, rundunar ‘yan sandan jihar Kano, a jiya ta bayar da tabbacin a shirye ta ke ta samar da isasshen tsaro a zaben cike gurbi da za a gudanar a yau a wasu sassan jihar. Kwamishinan ‘yan sandan da aka tura jihar domin daukar nauyin zaben, CP Muhammad Usaini Gumel, ya bayar da wannan tabbacin a jiya yayin da yake jawabi ga jami’an hukumar a hedikwatar hukumar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: