DIG. Ali Aji Janga Da Sauran Manyan Jami’an Tsaro Ne Ke Kula Da Sha’anin Tsaro A Zaben Gwamnan Adamawa

0 106

An tura mataimakin sufeto-Janar na ‘yan sanda (DIG), Ali Aji Janga, zuwa jihar Adamawa, acewar manema labarai, an ga yadda jami’an ‘yan sanda a wasu muhimman wurare a Yola, babban birnin jihar, musamman a kusa da ofishin INEC.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Sulaiman Nguroje ya fitar, ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammed Barde, wanda ya fara aiki a matsayin kwamishinan zabe, ya karbi DIG da sauran manyan jami’an da suka isa jihar.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a jihar Adamawa ta raba wasu muhimman kayyakin gudanar da zabukan gwamnoni da na majalisun jihohi.

Da yake jawabi ga manema labarai yayin rabon kayan a ranar Juma’a, kwamishinan zaben Hudu Yunusa Ari ya ce za a gudanar da zaben ne a rumfunan zabe 69.

Haka zalika ya kara da cewa za’a Kula da tsaro domin zaɓen da aka shirya gudanarwa a yau.

Leave a Reply

%d bloggers like this: