Jam’iyyar PDP a Bauchi ta lashe dukkanin kujerun shugabancin kananan hukumomin jihar 20 da kuma kujerun kansiloli 323, a zaben da aka gudanar na ranar asabar da ta gabata.

 A jiya lahadi ne zababbun chiyamomin da mataimakansu, suka karbi shaidar lashe zaben daga shugaban hukumar shirya zabukan jihar Dahiru Tata, a helkwatar hukumar.

Zababbun shugabannin sunsha rantsuwar aiki ne a hannun mai shari’a Hamidu Kunaza, wanda ya wakilci babbar alkaliyar jihar Mai shari’a Rabi Umar.

A jawabinsa yayin bikin rantsuwar, gwamna Bala Mohammad ya gargadesu da aika laifukan cin hanci da rashawa a yayin gudanar da aiki.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: