Ramuwar Gayya: Wasu mutane sun kashe mutum 8 a jihar Kaduna

0 68

A wani harin Ramuwar Gayya, wasu mutane sun kashe mutane 8 a karamar hukumar Zangon Kataf na Jihar Kaduna.

Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida Mista Samuel Aruwan, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya bayyana cewa harin ramuwar gayyana ne kan harin da aka kai kyauyen Jankasa dake karamar hukumar.

A jiya Litinin ne aka kai hari kyauyen inda aka kashe wani mutum mai suna Yakubu Danjuma, tare da kashe mutane 34 a kyauyen Madamai na karamar hukumar Kaura ta jihar.

Gwamnan Jihar Malam Nasiru El-Rufa’i ya bayyana damuwarsa kan kisan, tare da addu’ar Allah ya jikan mutanen da suka rasu a sanadiyar rikicin.

Gwamnan ya bukaci Al’ummomin su kasance masu bin Doka da Oda, ta hanyar dakatar da daukar fansa.

Haka kuma ya umarci hukumomin tsaro su gudanar da bincike kan faruwar lamarin.

Kawo yanzu hukumomin tsaro suna cigaba da gudanar da bincike kan wuraren da hare-haren ya shafa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: