Uwargida Gwamna Ganduje tayi gangamin wayarda mata gameda illolin shaye-shayen migayun kwayoyi

0 53

Mai Dakin Gwamnan Jihar Kano Farfesa Hafsat Umar Ganduje ta kaddamar da gangamin yaki da shaye-shayen migayun kwayoyi tare da kaddamar da Jakadu Mata wanda zasu yi yaki da matsalar a jihar.

Ofishin Mai Dakin Gwamnan Jihar tare da Ma’aikatar Harkokin Mata da kuma Hadin Gwiwar Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa NDLEA ne suka shirya gangamin.

Da take Jawabi a wurin kaddamar da gangamin Hajiya Hafsat Ganduje, ta ce manufar kaddamar da gangamin shine domin a dakile matsalar shaye-shayen migayun kwayoyin a tsakanin Matasa.

Haka kuma ta yabawa Gwamnan Jihar bisa yadda yake bada fifiko ga fannin Lafiyar Jihar.

Kazalika, ta bukaci Matan Shugabannin Kananan Hukumomi 44 na Jihar da Matan yan Majalisar Wakilai 40 da kuma Matan Kwamishinonin Jihar sun sanya hannu wajen yaki da matsalar.

A jawabinta, Kwamishiniyar Ma’aikatar Mata da Jindadin Al’umma ta Jihar Dr Zahra’u Muhammad Umar, ta ce manufar shirya gangamin shine domin a dakile matsalar shaye-shaye a jihar baki daya a tsakanin Matasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: