Gwamnatin Sojin Guinea sun hana mambobinsu shiga takarar zaben kasar

0 68

Gwamnatin Sojin Guinea sun hana mambobinsu shiga takarar zaben kasar wanda za’a gudanar a nan gaba kadan domin komawa Demokradiya.

Gwamnatin kasar karkashin Jagorancin Colonel Mamady Doumbouya, ta bayyana cewa zata mika mulki ga gwamnatin rikon kwarya.

Gwamnatin rikon kwaryar tana karkashin Firaministan da kuma mambobin Majalisa, kuma ita ce wanda zata jagoranci harkokin mulkin.

Majalisar zata kunshi Mambobi 81 wanda aka zabo su daga sassa daban-daban wanda suka kunshi yan kasuwa, yan siyasa da shugabannin addinai da kuma kwararru.

An kuma bukaci kaso 30 ya kasance Mata, sannan akwai shugaban kasa da Mataimakinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: