Sama da ‘yan Najeriya miliyan 1 da dubu 800 ne aka kammala yiwa allurar rigakafin corona

0 71

Sama da ‘yan Najeriya miliyan 1 da dubu 800 ne aka kammala yiwa allurar rigakafin corona, watanni 6 bayan an fara yin rigakafin a kasarnan.

Daraktan zartarwa na hukumar lafiya matakin farko ta kasa, Dr Faisal Shu’aib, ya sanar da haka jiya a Abuja, a wajen taron manema labarai na kwamitin corona na shugaban kasa.

A cewar Faisal Shu’aib, akalla mutane miliyan 4 da dubu 734 da 769 aka yiwa rigakafin a zagaye na farko a Najeriya, ya zuwa ranar 26 ga watan Satumba.

Sai dai, Faisal Shu’aib yayi gargadin cewa babban laifi ne a samu wani wanda zai samu katin shaidar rigakafin ba tare da an yi masa rigakafin ba, kamar yadda saye da sayar da katin rigakafin ta bayan fage yake a matsayin babban laifi.

Yace gwamnatin tarayya ta samar da rigakafin a kyauta ga dukkan wadanda suka cancanta, inda ya yi gargadin cewa an dora kula da katin rigakafin a wuyan shugabannin asibitoci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: