Kungiyar gwamnonin jihohin arewa ta ce bata yadda dan yankin kudu ya shugabanci Najeriya ba

0 85

Kungiyar gwamnonin jihohin arewa ta yi watsi da matsayin takwarorinsu na kudanci da ke cewa sai lallai shugaban kasar na gaba ya fito daga kudancin Najeriya.

A lokacin wani taro da kungiyar gwamnonin arewan ta yi jiya, ta ce babu wanda zai tilasta wa yankin zaben shugaban kasa daga wani sashen kasarnan.

Matsayar gwamnonin na zuwa ne bayan a watan Yuli kungiyar gwamnonin kudancin kasarnan suka bukaci dole a basu dama mulki ya koma garesu domin tabbatar da adalci.

Gwamnonin Arewar na cewa matsayar takwarorinsu na kudanci kan harajin VAT alamace da ke nuna sun kasa gane bambanci harajin VAT da wanda ake tarawa lokacin cinikayya.

Kazalika, shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, yace gwamnonin kasarnan na jiran sakamakon hukuncin kotun koli kafin ta dauki wani mataki dangane da harin na VAT da ake takaddama akai.

Kayode Fayemi ya sanar da hakan lokacin da aka zanta da shi a gidan talabijin na Arise.

Leave a Reply

%d bloggers like this: