An kama wani ma’aikacin lafiya da baiwa yan fashin daji magani a jihar Katsina

0 131

Wani ma’aikacin lafiya a jihar Katsina mai suna Murtala Umar, yace ya jima yana duba ‘yan fashin daji tare da basu maganin harbin bindiga, duk da kasancewar yasan ‘yan fashin daji ne.

Da yake zantawa da manema labarai a helkwatar yansanda dake Katsina, inda ‘yansanda suka gabatar da shi a jiya da yamma, sai dai Murtala Umar, yace ‘yan fashin dajin sun takura masa ne ala tilas ya basu hadin kai.

Murtala Umar, dan shekara 34, yana da kemist a kauyen Tashar Yan Alewa dake karamar hukumar Danmusa ta jihar.

Kauyen na daya daga cikin inda mahara suka fi addaba amma lamarin bai taba shafarsa ba, wanda hakan ya jawo mazauna kauyen suka fara zarginsa kuma suka sanar da ‘yansanda.

Yace yana sane cewa ‘yan fashin daji ne amma kasancewar a ko da yaushe suna zuwa da bindigogi, bashi da yadda ya iya.

A dai wajen kuma, yansanda sun kuma gurfanar da wani gawurtaccen dan fashin daji mai suna Ibrahim Sama’ila.

Da yake zantawa da manema labarai, wanda ake zargin, da aka fi sani da Yellow, yace yana da hannun wajen aikata laifuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: