Ranar Mata: Majalisar Dinkin Duniya ta koka kan rashin daidaton maza da mata

0 85

Ranar 8 ga watan Maris din kowacce shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ta mata dungurungum, a wani yunkuri na samar da daidaito tsakanin matan da takwarorinsu maza, sakamakon fuskantar karancin wakilcin matan a kusan kowanne bangaren rayuwa.

Manufar ranar Mata ta duniya da ke gudana a kowacce ranar 8 ga watan Maris bai wuce fayyace rawar da suke takawa cikin al’umma ba, baya ga zaburar da su da nufin yin gogayya da takwarorinsu Maza a fannonin rayuwa da kuma kawo karshen kyama hantara ko kuma banbancin da suke fuskanta.

Wani rahoton baya bayan nan da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar, ya nuna yadda mata ke bukatar karramawa don samun kyakkyawar makoma mai cike da daidaito da zaman lafiya ba tare da nuna banbanci, kyama ko kuma aikata musu ta’addanci ba.

Taken bikin bana

Taken ranar matan ta bana shi ne ‘‘Mata a shugabanci, samar da daidaiton makoma a Duniyar Korona’’.

Rahoton Majalisar ya koka da cewa a kasashe 22 ne kadai ake da mata a matsayin shugabanni inda ake da kashi 24.9 na matan da ke wakilci a majalisun kasashe, wanda Majalisar ke cewa akwai bukatar shekaru 130 a nan gaba gabanin cimma nasarar samar da daidaiton mukamai tsakanin Mata da takwarorinsu Maza.

Rahoton ya kuma nuna irin rawar da Mata suka taka a yaki da Covid-19, inda ya ce akwai bukatar cikakken wakilcin mata a kowanne teburin zartas da hukunci ko kuma kulla shawara saboda irin gudunmawarsu ga al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: