Rashin Adalci Ne Bashin $800M Da Gwamnatin Shugaba Buhari Zata Ciyo, Kuma Ya Saba Wa Doka

0 62

Shugaban kasar ya aika da sakon jaje bisa rasuwar ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka da ‘yansandan Najeriya biyu dake yi musu rakiya yayin wani hari da ‘yan bindiga suka kai musu a karamar hukumar Ogbaru ta jihar Anambra.
A wani batun kuma, sanatan dake wakiltar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume, ya sha alwashin adawa da bashin dala miliyan 800 wanda gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta nemi ciyowa.
Shugaban kasar ya nemi majalisar dattawa ta amince masa ciyo bashin dala miliyan 800 domin samun kudaden tallafawa marasa karfi.
A cewar shugaban kasar, bashin da za ayi amfani da kudaden bashin da za a ciyo daga bankin duniya wajen tallafawa marasa karfi cikin talakawa bayan an janye tallafin man fetur.
Amma Ali Ndume a hirar da aka yi da shi a gidan talabijin na Trust ya kafe kan cewa bashin ya sabawa doka kuma babu adalchi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: