Mai bawa shugaban kasa shawara akan tsaro, Babagana Monguno, ya bukaci gwamnonin jihohi da suke tattaunawa akai-akai da masu ruwa da tsaki tare da kula da rikice-rikice kamar yadda ya kamata domin inganta tsaro a jihohinsu.
Babagana Monguno yayi kiran yayin shirin wuni biyu na kaddamar da sabbin zababbun gwamnoni da wadanda aka sake zaba na bana wanda kungiyar gwamnoni Najeriya ta shirya jiya jiya a Abuja.
Babagana Monguno, wanda ya samu wakilcin Joseph Dashwuep, wani babban ma’aikaci a ofishin mai bawa shugaban kasa shawara akan tsaro, ya kuma yi kira ga gwamnonnin jihohi da suke amfani da dabarar yaki da ta neman sulhu wajen magance rashin tsaro a jihohinsu.
Ya kuma shawarce su da suke ganawa da hukumomin tsaro da kungiyoyin fararen hula da kungiyoyin masu zaman kansu da ‘yan kasa da shugabannin gargajiya da na addinai.
Shima da yake jawabi, darakta janar na hukumar tsaro ta farin kaya, SSS, Yusuf Bichi, wanda yana daga cikin masu jawabi, ya shawarci gwamnoni da su dauki matakin gaggawa akan rahotannin sirri da na gargadi.
- Comments
- Facebook Comments