‘Yan Bindiga Sun Kashe Sama Da Mutane 30 A Gundumar Bwoi Dake Karamar Hukumar Mangu A Jihar Filato

0 94

‘Yan bindiga sun kashe sama da mutane 30 a gundumar Bwoi dake karamar hukumar Mangu a jihar Filato.
Kakakin ‘yansanda a jihar, Alfred Alabo, ya tabbatar da aukuwar lamarin cikin wata sanarwa.
Alfred Alabo yace kwamishinan ‘yansandan jihar, Bartholomew Onyeka, wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici ya bayar da umarnin a gaggauta aikawa da jami’an ‘yansanda zuwa wajen.
Yayi bayanin cewa saboda karfin makaman jami’an tsaro yayin kai dauki, ‘yan bindigar sun yi watsi da babura hudu da wata mota kirar Sharon da wasu makamai da aka yi amfani da su wajen aika-aikar.
Alfred Alabo ya tabbatar da cewa kwamishinan ‘yansandan jihar yayi kira ga mazauna yankin su kasance masu kaunar zaman lafiya inda ya kara da cewa hukumomin tsaro suna tsare-tsaren kama masu aikata laifuka.
Ya kuma yi kira ga mazauna yankin dake da wani bayani mai muhimmanci da su mikawa hukumomin tsaron domin daukar matakin gaggawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: