PDP Zata Karbi Mulki Daga Hannun Tinubu Bayan Watanni Shida Da Rantsar Da Shi

0 77

Wani babbban jigo a jam’iyyar PDP kuma kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Atiku Abubakar, Daniel Bwala, yace jam’iyyar PDP za ta karbe mulki daga hannun zababben shugaban kasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, watanni shida bayan an rantsar da shi.
Jam’iyyar ta PDP da Atiku Abubakar na kalubalantar hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC bisa ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.
Kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa za ta cigaba da shirye-shiryen sauraron karar da jam’iyyar PDP da kakakinta, Atiku Abubakar suka shigar a gobe.
Da yake magana a gidan talabijin na Arise dangane da karar, an tambayi Daniel Bwala akan abinda zai ce dangane da zargin da jam’iyyar APC ta yi na cewa jam’iyyar PDP na da dadadden tarihin magudin zabe mafi muni a kasarnan.
Daniel Bwala yace duk da kasancewar bazan musanta wannan zargin ba gabadaya, jam’iyyar PDP za ta yi kokarin wanke kanta ta hanyar neman afuwar ‘yan Najeriya tare da alkawarin gyarawa idan an sake basu damar komawa mulki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: