Rashin Bin Ka’idar Gini Ya Sanya Gwamnatin Nasarawa Rushe Gidaje 40

0 173

Kimanin gidaje 40 ne Gwamnatin jihar Nassarawa tace ta rushe, wadanda aka gina ba bisa ka’ida ba a hanyoyin ruwa, cikin kananan hukumomi 3 jihar.

Haka kuma tace an kama mutane 27, tare da gurfanar dasu a kotun tafi da gidanka, bisa take dokar tsaftar muhalli ta wata wata, da ake wanzarwa a jihar.

A wani labari kuma wata ambaliyar ruwa tayi sanadiyar rushewar  kimanin shaguna 6, hadi da wasu gidaje, biyo bayan saukar ruwan sama a jihar.

Babban jami’in kula da muhali na ma’aikatar muhalli da albarkatun kasa, Mallam Abubakar Mohammad, shine ya sanar da hakan gay an Jaridu, yayin ziyarar gani da ido, kan yadda shirin tsaftar muhalli ta wata wata ke gudana a Lafia, babban birnin jihar.

Yace gwamnati na daukar matakan ne a kokarin kawo karshen matsalar ambaliyar ruwa a jihar.

Haka kuma yace dabi’ar kunnen kashi da wadansu mutane keyi ga umarnin gwamnati, kan hani da yin gine gine a hanyoyin ruwa, itace ta sanya aka dauki matakin yin rusau.

Leave a Reply

%d bloggers like this: