Mai Martaba sarkin Hadejia Alhaji Dakta Adamu Abubakar Maje CON, ya ziyarci mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a fadarsa da ke birnin Kano.

Wannan dai ita ce ziyarassa ta farko da ya kai fadar Kano bayan Aminu Ado Bayero ya zama Sarki.

A cikin watan Maris din shekarar bana gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin Aminu Ado a matsayin sabon Sarkin Kano.

Aminu Ado Bayero wanda ɗa ne ga marigayi Sarki Ado ya zama sarki na 15 a jerin Sarakunan Fulani na Kano.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: