Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, yace halin rashin tsaro da kasar nan ke fuskanta abu ne da hukumomin tsaro za su iya magance shi.
Kwankwaso wanda ya taba rike mukamin Ministan tsaron Najeriya, kana jigo a jam’iyyar NNPP, ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala zaman majalisar zartarwa ta kasa na jam’iyyar NNPP a Abuja.
Rabi’u Musa, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 20203, yace matukar aka ba wa jam’iyyar su dama suna iya magance wannan matsala ta rashin tsaro a kasar nan. Kazalika Kwankwaso, jam’iyyar NNPP itace mafita ga ‘yan Najeriya, kasancewar jam’iyyun APC da PDP dukkanins sun gaza kawo sauyi ga al’ummar kasar nan.