Akalla maniyyatan Najeriya 50,000 ne za su yi aikin hajjin shekarar 2024 a kasar Saudiyya

0 231

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta ce akalla maniyyatan Najeriya dubu hamsin ne za su yi aikin hajjin shekarar 2024 a kasar Saudiyya.

Shugaban Hukumar NAHCON, Malam Jalal Arabi, shi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudanar a jiya a Abuja.

Arabi ya ce hukumar na kan hanyar gudanar da aikin Hajji cikin nasara, ko da kuwa kalubalen da ake fuskanta.

Ya nanata cewa musulman Najeriya za su gudanar da aikin Hajjin 2024 a adadin da babu wanda ya taba tunanin. Arabi ya ce, gwamnatin tarayya ta shiga tsakani ta hanyoyi da dama, musamman ma da wasu tsare-tsare na tallafa wa hukumar domin tabbatar da cewa al’amura sun tafi daidai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: