Gwamnan Namadi ya dakatar da kwamishinan ma’aikatar kasuwanci na jihar Jigawa

0 327

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar A. Namadi ya dakatar da kwamishinan ma’aikatar kasuwanci kuma mamba a majalisar zartarwa ta jihar, Alhaji Aminu Kanta, kan zargin wasu badakaloli a shirin ciyarwa na watan Ramadana da gwamnatin jihar take yi.

Hakan ya zo ne a wata sanarwar da sakataren gwamnatin jihar, Malam Bala Ibrahim ya sanyawa hannu. Sanarwar ta bayyana hakan a matsayin yunkurin tabbatar da kididdigar da kuma lura da kudaden al’umar jihar ta Jigawa.

Jawabin ya bayyana umurnin gwamnan na sakataren gwamnatin ya mika takaddar dakatarwar a madadin gwamnatin jihar. Ya kara da cewa, An dakatar da kwamishinan ne bisa zarginsa da hannu wajen karkatar da kudaden ciyarwar buda baki a karamar hukumar Babura.

Leave a Reply

%d bloggers like this: