Jigawa Mayan Labarai Sawaba Security

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Lakume Rayuka A Jigawa

Rundunar yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da kisan manoma uku, a wani rikici da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a kauyen Adiyani dake karamar hukumar Guri dake jihar.

Kakakin rundunar SP Abdu Jinjiri, shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai, inda yace lamarin ya auku ne a ranar juma’a, da misalin karfe 1 da mintuna 35 na rana.

Jinjiri yace rikicin ya soma ne, bayan da kunshin wasu manoma sukayi tattaki zuwa cikin jejin domin kaiwa makiyayan hari, bisa zargin lalata musu amfanin noma, sai dai jami’ansu sunyi nasarar dakatar da manoman daga daukar doka a hannu.

Yace rukunin jami’ansu, da kuma rundunar Operation Salama, karkashin kwamandan yankin sun isa wurin, inda suka mika wadanda aka raunata asibiti, har ma likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.

Sannan jinjiri yace an umarci jami’an da su bi diddigi domin kame masu hannu a rikicin.

Haka kuma yace kwamishinan yan sandan jihar, ya ja kunnen manoman bisa daukar doka a hannu.

Sawaba FM

Our focus is to educate, entertain, inform and enlighten the populace, investigate for truth as a credible source of information.
Follow Me:

Related Posts

%d bloggers like this: