Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbanjo yace yan najeriya shirye suke da biyan kudin wutar lanyarki idan aka inganta tsarin bada wutar.
Osibanjo ya bayyana hakane a wani taron karawa juna sani da aka gudanar ta kafar internet, na ganin dorewar wutar lantarkin bayan shudewar annobar covid19 wanda Emmanuel Chapel ya shirya a jiya lahdi a babban birnin tarayya Abuja.
- Sanata Shehu Buba zai horas da matasa 250 kan sana’ar gyaran takalma a jihar Bauchi
- Cibiyoyin kula da lafiyar kafafu da hannaye a Najeriya ta bude sabon ofishi a Kano
- Gwamnan Namadi ya amince da Mai Martaba Sarkin Kazaure a matsayin Amirul Hajj na jihar Jigawa
- Dalibai 41,000 da ba su kai shekara 16 ba sun yi rajistar JAMB ta shekarar 2025
- Za a fara gudanar da jarrabawar WAEC da NECO ta hanyar na’ura wato CBT
- INEC ta jaddada gyaran kundin tsarin mulki da dokokin zaɓe
Yace ba gaskiya bane cewa da ake yan najeriya basa san biyan kudin wuta, ya kara cewa yan kasar basa farin ciki tsawon shekaru ganin yadda ake gudanar da harkokin bada wutar.
Mataimakin shuganan kasar ya kuma yi magana bisa kasafin kudin shekarar 2020 a harkar lafiya.
Osibanjo yace kasafin kudin shekarar 2020 da aka ware a fannin lafiya shine mafi yawa da aka taba warewa shekaru biyar da suka wuce.