Lafiya Mayan Labarai Rayuwa

Maganar Shugaba Buhari Bayan Nijeriya Tayi Bankwana Da Polio

Shugaba muhammadu Buhari ya taya yan najeriya murna biyo bayan bankwana da kasar tayi daga cutar shan inna, yayin nuna godiyarsa ga wanda suka taimaka na gida dana waje, bisa jajircewarsu na ganin sun raba kasar da cutar yaran.

A jawabinsa shugaban kasa ta bakin mataimaki na musamman wajen yada labarai da hulda da jamaa, Garba shehu, yace wannnan nasara zata sanyaya ruhin yan kasar.

 • Bara Aka Hana Ba Karatun Al’Ƙurani ba – Aliyu Tilde
  Shahararren malamin nan Dakta Aliyu Tilda ya bayyana cewa haryanzu mutane basu fahimci me ake nufi da Almajiranci ba, inda ya ce Ƙoƙarin da gwamnonin Arewa ke yi na hana baran yara da sunan almajirci da alama bai yi wa masu ci da hakkin wadannan yaran dadi ba. Akwai kuma ƴan siyasa waɗanda don ba […]
 • Fanni Shari’a Ya Samu Sabon Sauyi A Jigawa
  Wannan yana cikin Doka Mai Namba 5 na shekarar 2020 da Babban Alkalin Jiha, kuma shugaban Majalisar Hukumar Shari’a Hon Aminu Sabo Ringim, ya sanyawa hannun.
 • Cacar baka tsakanin Ministan Buhari da Majalisa na sake Daukar Zafi
  Kafin hakan dai an bayyana cewa a ranar talata data gabata ne ministan yaki ya nemi afuwar majalissar saboda ya daga musu murya a zuwansa majalissar domin yin bayani kan shirin Gwamnatin tarayya na daukar mutane Dubu 774 a wani sabon tsarin da take kokarin farawa a fadin kasar nan.
 • Za a Dawo da karbar haraji kan gidajen haya da Takardar shaidar mallakar gidaje
  hukumar ta bayyana cewa daga yanzu ya zama wajibi ake biyan kudin harajin gidajen haya dana takardun mallakar gidaje.
 • Farfesa Maqariy ya ajiye aikin Jami’a
  Bayan kwashe shekaru yana aikin koyarwa a Jami’ar Bayero dake Kano, babban limamin masallacin birnin tarayya dake Abuja Farfesa Ibrahim Ahmad Said Maqariy (Hafizahulla) ya ajiye aikinsa domin maida hankali wajen hidimtawa Addini.Bayan Jami’ar ta Bayero ta amince da ajiye aikin malamin, a wata takarda dake dauke da amincewar hukumar makarantar. Malam Maqarin ya bayyana […]
 • Jihar Jigawa zata Tura Matasa Karatun Likita Kasar Waje
  Wannan shiri na yayan talakawa ne kawai wadanda suka gama karatun secondary a makarantun gwamnati kuma za a zakulo yaran bisa chancanta kawai.

Haka kuma Ya yabawa maza da mata da suka bada gudummawa a fannin lafiya, wanda ya alakanta nasarar da jajircewarsu da goyon bayansu wajen kawo karshen jinyar.

Buhari yace wannan nasara ba ita kadai alummar kasar suka cimmaba a lokacin mulkinsa, kuma wannan abune da baza a taba mantawa dashiba a idan aka tina mulkinsa, wannan nasara ta kawo daidaito wajen ciyar da kasar gaba a fannin lafiya tun a shekarar 2015.

Sawaba FM

Our focus is to educate, entertain, inform and enlighten the populace, investigate for truth as a credible source of information.
Follow Me:

Related Posts

%d bloggers like this: