Rundunar ƴan sandan jihar Neja ta kama wani mutum bisa zargin yana garkuwa da mutane

0 227

A halin da ake ciki kuma, rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta ce ta kama wani mutum mai suna Bala Mohammed da ke kauyen Wawa a karamar hukumar Burgu ta jihar, bisa zargin yana garkuwa da mutane.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Minna.

Abiodun ya ce a ranar 30 ga watan Nuwamba da misalin karfe 7 na safe, rundunar ‘yan sandan ta samu rahoton cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun rubuta wasika, inda suka yi barazanar kai hari ga mutanen kauyen Kampani-Jibrin ta hanyar Nasko a karamar hukumar Magama ta jihar.

Kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewa, yayin gudanar da bincike an gano bindiga guda daya da wayoyin hannu hudu da wasikun barazana guda hudu da layukan waya 15 laya da kuma kudi da ake zargin na bogi ne a gidansa.

Ya kara da cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa na kasancewa dan tawagar mutane hudu ne na wata kungiyar masu garkuwa da mutane wadanda a yanzu suka tsere.

Leave a Reply

%d bloggers like this: