Rundunar ƴansanda a jihar Legas ta ce dalibai 2 sun mutu sannan 12 a wani hatsarin mota

0 170

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta ce dalibai biyu sun mutu sannan 12 sun jikkata a wani hatsarin da ya afku jiya da rana a wata makarantar da ke Ojodu-Berger a Legas.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Adekunle Ajisebutu, ya fitar jiya, ta ce wadanda abin ya shafa dalibai ne na makarantar Bab Fafunwa Millennium, Ojodu, wacce a baya ake kiranta da suna Ojodu Grammar School.

Alkaluman ‘yan sandan sun sha banban da na wasu shaidu da suka ce akalla yara ‘yan makaranta 13 ne suka mutu a hadarin.

Ajisebutu ya ce da misalin karfe 2 da kwata na rana wata mota kirar DAF da wani Bolaji Kabiru ke tukawa ta take wasu masu tafiya a kasa, lamarin da ya yi sanadin jikkatar mutane.

Ajisebutu ya ce an tura jami’an kula da tituna da sauran masu kai dauki zuwa wajen da hadarin ya auku.

Ya ce an kai daliban da suka jikkata zuwa asibitin God’s Apple City; da asibitin Saint Michael; da asibitin daukin gaggawa na Jihar Legas.

Leave a Reply

%d bloggers like this: