Rundunar Sojin Najeriya ta musanta rahotan cewa jami’anta sun yi murabus ne saboda cin hanci da rashawa

0 98

Rundunar Sojin kasar nan ta musanta rahotannin da kafafen yaɗa labarai na baya-bayan nan da ke nuna cewa jami’anta sun yi murabus daga aikinsu ne saboda cin hanci da rashawa, da rashin ɗa’a, da kuma rashin walwala.

A makon nan ne dai wasu kafofin watsa labaran suka yi ta naƙalto wani rahoto da ke nuna yadda sojoji fiye da guda 1000 suka yi murabus bisa zarge-zargen rashin jin daɗin aiki da rashawa da cin hanci “da ya yi wa aikin katutu”.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana waɗannan iƙirari a matsayin karya da kuma yunƙurin ɓata mata suna da gangan.

A cewar rundunar, rahotannin an yi su ne domin haifar da saɓani da kuma ɓata tarbiyar jami’anta.

Rundunar Sojin ta kuma bayyana ci gaba da jajircewarta na jin dadin ma’aikatanta a ƙarkashin jagorancin babban hafsan sojin ƙasar, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja. Daga ƙarshe rundunar ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su tantance bayanai kafin a buga su don hana yaɗa labaran da ba su da tushe balle makama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: