Wani mutum ya nutse a kogin Hadejia

0 138

Wani mutum mai suna Sulaiman Potiskum mai shekaru 55 ya nutse a ruwa, bayan ya yi iyo a wani kogi da ke karamar hukumar Hadejia a jihar Jigawa.

Kakakin hukumar tsaron farin kaya ta kasa NSCDC Badaruddeen Tijjani, na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar jiya a Dutse.

Tijjani ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 9:45 na safe, lokacin da marigayin ya tafi ninkaya a cikin kogin.

Ya ce tawagar jami’an binciken gawarwakin da masu ruwa da tsaki na yankin sun ceto mutumin, inda ya ce daga baya jami’an lafiya a babban asibitin Hadejia suka tabbatar da mutuwarsa. Kakakin ya shawarci mazauna jihar da su daina yin iyo ko kamun kifi a cikin koguna saboda karuwar ruwan sama ya yi kamari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: