Rundunar sojin saman Najeriya ta fara jigilar kayayyakin agaji a Maiduguri

0 96

A jiya ne rundunar sojin saman kasar nan ta ce ta fara jigilar kayayyakin agaji ta sama ga wadanda ibtila’in ambaliyar ruwa a Maiduguri ya rutsa da su, domin cika aikinta na bayar da agajin soji ga hukumomin farar hula.

Hukumar NAF ta kuma bayyana cewa, kayayyakin da hukumar hana fasa kwauri ta kasa (NCS) ta bayar, na da nufin rage wahalhalun da ambaliyar ruwa ta haifar, wanda ya kawo cikas ga harkokin yau da kullum na mazauna Maiduguri, da lalata dukiyoyinsu, da kuma raba miliyoyi.

Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a da Watsa Labarai na NAF Captain Kabiru Ali, ya ce sun samu kason farko na kayayyakin agajin, wanda ya kunshi buhu 300 na shinkafa mai nauyin kilogiram 50, an samu nasarar isar da su zuwa Maiduguri ta hanyar jirgin sama.

Ya kara da cewa manyan manyan motoci da NAF suka bayar an yi amfani da su wajen jigilar kayan zuwa gidan gwamnatin jihar Borno domin rabawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: