Da sanyin safiyar yau ne hukumar NNPC ta fitar da kiyasin farashin man fetur da aka samu daga matatar man Dangote a gidajen sayar da man da ke fadin kasar nan, inda ta jaddada cewa bisa tanadin dokar masana’antar man fetur (PIA), ba gwamnati ce zata kayyade farashin man fetur ba.
A cikin takardar da aka makala, hukumar NNPC ya bayyana cewa man da ake samu daga matatar Dangote za a sayar da shi kan Naira 950.22 kan kowace lita a Legas; N960.22 a Oyo; N980.22 a Rivers; N992.22 a Abuja; N999.22 a Kaduna; N999.22 a Kano; N999.22 a Sokoto da kuma N1,019 a Borno, bisa tsarin farashi na watan Satumba.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar NNPC ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa matsalar karancin man fetur da kuma dogayen layukan da ake fama da su a gidajen man za su bace nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.
Kamfanin mai na kasa ya kuma jaddada cewa, ba za a kayyade farashin man fetur daga matatar man fetur din NNPC ko Dangote ba, yana mai cewa daga yanzu yan kasuwa ne za su kayyade farashin man fetur.