Labarai

Rundunar Sojin Saman Najeriya ta lalata maboyar yan bindiga a kyauyen Kambari da ke karamar hukumar Karim Lamido ta jihar Taraba

Rundunar Sojin Saman Najeriya ta lalata Maboyar yan bindiga a kyauyen Kambari da ke karamar hukumar Karim Lamido ta Jihar Taraba.

Manema Labarai sun rawaito cewa hare-haren Saman da Sojojin suke kaiwa tsawon kwanaki 3 ya yi sanadiyar kashe yan bindiga da dama.

An rawaito cewa an kashe wasu mutane 3 a lokacin da suke kan Babura a lokacin harin saman a yankin Kwatan Nanido da ke karamar hukumar Gassol ta Jihar.

Yan bindigar sun yi sansani a yankin Kambari tsawon watanni 2, inda suka addabi yankin da sace-sacen mutane domin neman kudin fansa da kuma kaiwa hare-hare kan kyauyika a kananan hukumomin Gassol da Karim Lamido.

An yi kokarin jin ta bakin Kakakin rundunar sojan saman Najeriya amma abin ya ci tura.

Kakakin yan sandan Jihar Taraba DSP Usman Abdullahi, ya ce bashi da Masaniya kan hare-haren da Sojojin saman suka kai.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: