Labarai

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Jigawa ta ce kimanin mutane 595 ne suka mutu a sanadiyar cutar Amai da Gudawa wanda ta harbi mutane dubu 21,877

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Jigawa ta ce kimanin mutane 595 ne suka mutu a sanadiyar cutar Amai da Gudawa wanda ta harbi mutane dubu 21,877 a Jihar cikin shekarar 2021.

Babban Sakatare a Ma’aikatar Dr Salisu Mu’azu, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Dutse.

A cewarsa, kaso 100 na bullar cutar yana da alaka da rashin tsaftar muhalli da na Jiki, inda ya ce Jihar ta samu gagarumar nasara wajen samar da tsaftaccen ruwan sha a Jihar, amma duk da hakan an samu asarar rayuka.

Haka kuma ya ce domin rage adadin mutanen da suke mutuwa a sanadiyar cutar, Ma’aikatar sa, ta sanya kwamatin kota kwana domin rage adadin mutanen da cutar ka iya hallakawa a shekarar 2022.

Dr Salisu Mu’azu ya ce cikin shekarar 2021 da ta gabata an samu mutane dubu 946 da 325 da aka musu rigakafin cutar a Birnin Kudu da Dutse, sai kuma mutane dubu 904 da 169 da aka musu rigakafin cutar a karamar hukumar Hadejia.

Babban Sakataren ya ce daga cikin mutanen da aka yiwa rigakafin cutar, Jihar ba ta samu rahotan Mace mai juna biyu da ta mutu ba.

Kazalika, ya ce Ma’aikatar ta kashe kimanin Naira Miliyan 8 da dubu 700 a shekarar 2021, wajen daukar Direbobin haya domin kaiwa mutane Asibiti.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: