Labarai

Alhaji Aliko Dangote ya bada tabbacin cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne zai bude matatar mansa kafin karshen wa’adin sa na shekarar 2023

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote, ya bada tabbacin cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne zai bude Matatar Mansa kafin karshen wa’adin sa na shekarar 2023.

Dangote ya bayyana hakan ne a jiya lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawa da Shugaba Buhari.

Alhaji Aliko Dangote, wanda aka tambayeshi kan yaushe ne Matatar Mansa zata fara aiki, ya ce da Izinin Allah kafin karewar wa’adin Shugaba Buhari za’a bude Matatar Man.

Dangote ya ce Matatar zata samar da ayyukan yi, da biyan haraji ta yadda gwamnati zata samu kudaden shiga domin ciyar da kasa gaba.

Manema Labarai sun tambayi Dangote ko karancin Sinadarin Potash a sanadiyar rikicin Russia da Ukraine zai shafi sabuwar Matatar tasa, sai ya ce kasashen biyu suna samar da kaso 26 cikin 100 ne kawai na Sinadarin a Duniya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: