Hukumar Hana Fasakwafri ta Kasa kwastam ta sanar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin bude karin iyakokin kasar nan guda hudu

0 72

Hukumar Hana Fasakwafri ta Kasa kwastam ta sanar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin bude karin iyakokin kasar nan guda hudu.

Iyakokin sun hada da Idiroko dake Ogun, Jibiya dake Katsina, Kamba dake Kebbi da Ikom dake Cross River.

Idan za a iya tunawa de a watan Agustan 2019, Shugaba Buhari ya rufe dukkan iyakokin kasa don dakile shigo da makamai da shinkafa daga kasashen Afrikan dake makwabtaka da Najeriya.

Kuma a shekarar 2020, bisa shawaran ministar kudi, shugaban kasa ya sassauta yace a bude na Seme, llela, Maigatari da Mfum.

Hukumar ta bayyana haka a wata sanarwa mai dauke da Sahannun Mataimakin Kwantiloran Hukumar E.I Edorhe wanda aka rabawa manema labarai.

Sanarwar ta ce hukumar ta Kwastom zata bude iyakokin ne biyo bayan umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na ranar 16 ga watan Disamba na shekarar 2020.

Leave a Reply

%d bloggers like this: