Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce an kashe akalla ‘yan ta’adda biyu a jiya tare da kwato muggan makamansu da layukan su da kuma alburusai

0 61

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce an kashe akalla ‘yan ta’adda biyu a jiya tare da kwato makamansu da layukan su da kuma alburusai.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isah ne ya bayyana haka a yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar rundunar ta Katsina.

Ya ce an kashe ‘yan ta’addan ne biyo bayan kiran da rundunar ta samu cewa sun kai hari kauyen Tsamiyar Gamzako da ke karamar hukumar Kafur.

Tare da yin garkuwa da wata mata ‘yar shekara 30 da yarta ‘yar watanni 15.

Isah ya ce hakanne yasa suka hada tawagar ‘yan sanda da ‘yan banga, kuma suka samu nasarar kama ‘yan ta’addan da muggan makamai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: